Zaɓen 2027: Ƙungiyar Arewa maso Yamma ta ce Yari zai zama babban jigon dabarun yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC
Ƙungiyar Northwest Progressives Forum (NPF), wadda ke sahun gaba wajen tallafa wa harkokin siyasa, ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da su naɗa tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai ci, Abdulaziz Yari, a matsayin Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa (PCC) na jam’iyyar a zaɓen 2027.
Ƙungiyar ta ce naɗa Yari zai bai wa APC zurfin dabarun siyasa, ƙwarewar harkokin siyasa, ƙarfin tattara magoya baya a matakin ƙasa da kuma damar haɗa ƙungiyoyi da jam’iyyun siyasa, waɗanda ake buƙata domin tabbatar da gagarumar nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
A cikin wata sanarwa da mai kula da harkokin ƙungiyar na ƙasa, Comrade Tukur Aliyu Dambatta, da Sakataren Yada Labarai na Ƙasa, Alhaji Sani Kamba, suka sanya wa hannu, NPF ta ce kusantar lokacin zaɓen 2027 na buƙatar “dabarun da aka gwada, babban jari na siyasa da kuma ingantaccen ƙarfin tattara jama’a a matakin ƙasa.”
A cewar ƙungiyar, Arewa maso Yamma na ci gaba da kasancewa yankin da ya fi muhimmanci a fagen zaɓe a Najeriya, kasancewar yankin na da mafi yawan masu kada kuri’a a ƙasar. Saboda haka, ƙarfafa goyon bayan APC a yankin na da matuƙar muhimmanci ga duk wani yunƙuri na samun gagarumar nasara a zaɓen shugaban ƙasa.
NPF ta yi nuni da cewa Sanata Yari na da nauyin siyasa da kuma kusanci da jama’a a matakin ƙasa da ake buƙata domin ƙarfafa goyon bayan APC a dukkan jihohi bakwai na Arewa maso Yamma, wato Zamfara, Kano, Kaduna, Katsina, Jigawa, Sokoto da Kebbi.
Ƙungiyar ta bayyana Yari a matsayin ƙwararren jigon siyasa mai “babban daraja, amintattun alaƙun siyasa da farin jini” a yankin, tana mai cewa dimbin hanyoyin sadarwarsa na siyasa za su iya zama muhimmin ginshiƙi ga yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC.
Haka kuma, ƙungiyar ta jaddada ƙwarewar Yari a harkokin siyasa, inda ta kawo misalin shekaru takwas da ya yi yana Gwamnan Jihar Zamfara, lokacin da ta ce ya nuna ƙwarewa wajen shugabanci da gudanar da mulki, da kuma lokacin da ya jagoranci Nigeria Governors’ Forum (NGF) a matsayin shugabanta.
A cewar NPF, ƙwarewar Yari a matsayin Shugaban NGF ta ba shi damar yin aiki wajen samar da matsaya guda tsakanin gwamnoni, diflomasiyyar siyasa tsakanin jam’iyyu da kuma tafiyar da muradu masu sarkakiya na siyasa a jihohi 36 na Najeriya.
Ƙungiyar ta kuma nuna cewa kasancewar Yari Sanata mai ƙwarewa a Majalisar Dattawan Tarayyar Najeriya ya ba shi kyakkyawar alaƙa da hukumomin Majalisar Ƙasa, tare da ingantattun hanyoyin sadarwa da masu ruwa da tsaki a siyasar ƙasa.
Dangane da shirya yakin neman zaɓe da tattara albarkatun da ake buƙata, NPF ta ce Yari ya sha nuna ƙwarewar tattara ma’aikata, gina ingantattun tsare-tsare da kuma haɗa masu ruwa da tsaki daban-daban domin cimma manufa guda.
Ta ce irin wannan ƙarfin tsari zai kasance muhimmi wajen gudanar da ayyukan Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa, musamman a zaɓe mai muhimmancin siyasa kamar na 2027.
Ƙungiyar ta kuma bayyana Yari a matsayin ɗan jam’iyya mai biyayya da haɗa kan jama’a, wanda zai iya samar da gada tsakanin shugabannin jam’iyya, gwamnoni, ‘yan majalisa da magoya bayan jam’iyya a matakin ƙasa.
Ta ce ƙwarewarsa wajen gina ƙawance za ta kasance mai matuƙar amfani a wannan lokaci da haɗin kai da fahimtar juna a cikin jam’iyya da kuma faɗaɗa haɗin gwiwar siyasa ke da muhimmanci ga damar APC ta samun nasara a zaɓe.
Saboda haka, NPF ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi la’akari da “lissafin siyasar 2027” tare da damƙa jagorancin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ga gogaggen ɗan dabarun siyasa daga Arewa maso Yamma.
Haka kuma, ta yi kira ga Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC) na APC da dukkan gwamnonin APC da su mara wa Yari baya domin samun wannan matsayi, tana mai cewa fitowarsa zai taimaka wajen samar da haɗaɗɗiyar, ƙarfaffiyar kuma ta ƙasa baki ɗaya hanyar gudanar da yaƙin neman sake zaɓen Shugaba Tinubu.
“Zaɓen 2027 na buƙatar ingantattun dabaru. Sanata Abdulaziz Yari a matsayin DG na PCC zai samar da gada tsakanin mai kada ƙuri’a a matakin ƙasa da kuma nasarar ƙasa baki ɗaya,” in ji ƙungiyar.
NPF ta sake jaddada cewa kiran nata ya samo asali ne daga ƙudurinta na ƙarfafa haɗin kan yankin, tabbatar da haɗin kan ƙasa da kuma ci gaba da samun nasarar APC a fagen zaɓe.